12 Faburairu 2020 - 06:36
Mali: Gwamnati Za Ta Tattaunawa Tare Da 'Yan Tawaye

Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana cewa akwai tuntubar juna tsakaninsu da yan tawayen kasar da zummar gudanar da tattaunawar da zata haifar da zaman lafiya bayan daukar dogon lokaci ana kashe mutane a sassan kasar.

(ABNA24.com) Shugaban Kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita ya bayyana cewa akwai tuntubar juna tsakaninsu da yan tawayen kasar da zummar gudanar da tattaunawar da zata haifar da zaman lafiya bayan daukar dogon lokaci ana kashe mutane a sassan kasar.

Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Keita ya bayyana cewa ya nada tsohon shugaban kasar Dioncounda Traore domin tattaunawa da Yan bindigar domin kawo karshen asarar rayukar da ake tafkawa a kasar.

Kungiyoyi da dama sun dade suna kira ga gwamnatin Mali da ta shiga tattauna da Yan tawayen domin ganin sun ajiye makamansu, da kuma rungumar zaman lafiya, cikin su har da kungiyar ICG.

Kasar Mali ta fuskanci matsaloli masu tarin yawa a arewacin kasar, tun bayan bullar ‘yan tawaye, inda daga bisani kuma barazanar tsaroa yankin ta kara kamari bayan bullar kungiyoyi masu dauke da makamai da ke da’awar jihadi.




/129